ABNA24 : Har ila yau sanarwar ta kunshi cewa; kasar ta Rasha za kuma ta samar da kudade ga kasashen tarayyar da suke da sha’awar sayen allurar rigakafin.
Tarayyar Afirkan tana fatan ganin cewa adadin allurar rigakafin da ta saya daga Rasha za ta taimaka wajen yi wa kaso 60% na mutanen nahiyar rigakafi idan aka hada da wani adadin da ya kai miliyan 270 da ta shirya saya daga kamfanonin Johnson and Johnson da Pfizer Astra Zeneca.
Mutanen da su ka kamu da cutar covid-19 a nahiyar Afirka sun haura 3.79, wadanda su ka mutu kuwa sun kai 100,294, kamar yadda hukumar da ke fada da cutuka masu yaduwa a nahiyar ta Afirka ta bayyana.
342/